News
Gwamnatin Najeriya Za Ta Ƙaƙaba Sharudai A Twitter, Facebook, WhatsApp, Da Sauran Kafofin Sadarwa Na Zamani

Daga Yasir sani Abdullah
Lai Mohammed ya bayyana cewa Najeriya na yin gyaran fuska ga dokar yada labarai ta kasa da kuma ka’idojin yada labarai don tabbatar da cewa duk shafukan yanar gizo da ke aiki a kasar sun cika sharuddan da aka gindaya kamar yadda aka yi da Twitter.
“Duk abin da ya shafi Twitter zai shafi duk sauran kafafen sada zumunta, walau WhatsApp, Facebook ko wani,” in ji Ministan.
Ya ce an dakatar da Twitter a Najeriya ne saboda ya zama dandalin zabi ga masu son tada zaune tsaye a kasar, da haifar da rashin hadin kai da kuma zafafa harkokin siyasa.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a birnin Alkahira a wata ganawa da takwaransa na Masar, Dr Amir Talaat.