Kotun Jihar Bauchi ta ɗaure wani mutum tsawon shekara biyu mai suna Mohammed Magaji Ali bayan samunsa da laifin cin amana na kuɗi kimanin naira dubu ɗari shida da hamsin.
Hukumar EFCC a Najeriya ta wallafa cewa tun da farko wani mutum ya kai wa Mohammed Magaji shanu ya kula da su, amma sai ya kiwata su ya kuma sayar da su.
Hukumar ta bayyana cewa bayan an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.