News
Kotu ta bada umarnin kamo jarumin fim ɗinHausa, Sadiq Sani Sadiq
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kotun shari’ar Musulunci da ke Hotoro Masallacin Juma’a a Jihar Kano ta bayar da umarnin kamo mata Jarumin wasan Hausan, Sadiq Sani Sadiq.
Jaridar indaranka ta jiyo cewa wani mai shirya fina-finai, Aliyu Muhammad Hannas ne ya shigar da ƙarar a gaban kotun, inda ya ke ƙorafin cewar ya baiwa jarumin kuɗi domin ya yi masa aikin film, amma yaƙi zuwa don yin aikin.
Mai ƙarar ya kuma yi ƙorafin cewa ƙin yi aikin da Sadiq ya yi ya ja masa asara mai yawa.
Alkalin Kotun, Maishari’a Sagiru Adamu, yace Sadiq ya bijirewa umarnin kotu duk da sammacin da aka bashi, tare da liƙe masa sammacin a bangon gidansa, amma yaki halartar zaman kotun.
Shine sai ya baiwa dan sandan kotun umarnin kamo jarumin a duk inda yake zuwa gaban kotun.
Kotun tace da zarar an kamo jarumin wasan Hausan za a cigaba da zaman sauraren shari’ar.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Sadiq ya ce ba mai shirya fim ɗin ba ne ya bashi kuɗin kai tsaye.
Sadiq ya ƙara da cewa Naira dubu ɗari a ka bashi a matsayin wani ɓangare na kuɗin kwantaragin fim ɗin.
In da ya ce shi ba cinye masa kuɗi ya yi ba, hasali ma bai san ko wanene mai fim ɗin ba tunda ba kai tsaye su ka kulla yarjejeniya ba.