News
An kashe sarki da dogarai aka kone gawarsu a Najeriya
Daga kabiru basiru fulatan
A makon da ya gabata wasu ‘yan bindiga da ba a sansu ba sun kashe basaraken gargajiya na kauyen Agodo da ke karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, inda kuma suka kona shi tare da dogarawansa kurmus.
Rahotanni sun ce maharan sun kashe tare da kone Kabiesi Oba Odetola da dogaransa hudu, jim kadan da shigar basaraken da tawagarsa garin da kusan karfe goma sha daya na safiyar jiya Litinin 24 ga watan Janairun 2022.
Bayanai na nuna cewa wannan shi ne karo na biyu da irin wannan abin takaici ya auku a garin cikin ‘yan watannin nan.