News
APC mai mulkin Najeriya za ta rantsar da shugabanni a jihohi, wane ɓangare ne zai samu nasara?
Daga
muhammad muhamad zahraddin
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta rantsar da shugabanninta na jihohi 35 ranar Alhamis yayin da take cikin rikici a jihohin ƙasar da dama.
Lamarin na zuwa ne bayan kusan wata huɗu da aiwatar da zaɓukan shugabannin a matakin jihohi, waɗanda suka haifar da ɓangarori a cikin jam’iyyar daban-daban.
Wasu rahotanni da BBC ba ta tabbatar ba na cewa akwai yiwuwar shugabannin da za a rantsar na ɓangaren gwamnoni ne, abin da ke nufin ɓangarorin da wasu ‘yan Majalisar Dattawa da ministoci ke mara wa baya za su sha kaye a wurin rantsuwar.
Bikin zai gudana ne a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja babban birnin ƙasar, inda tuni aka jibge jami’an tsaro.
Daga cikin jihohin da suke fama da rikici akwai Kano da Kebbi da Zamfara da Bauchi da Kwara da Osun da Delta da Rivers.
Sai dai babu tabbas game da abin da zai faru da wasu jihohin da rikicinsu ke gaban kotu yanzu haka.
A wasu jihohin kamar Kano, ɓangaren da ke samun goyon bayan Sanata Ibrahim Shekarau ya zaɓi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaba, yayin da ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas.
Sai dai a ƙarar da ɓangaren Ganduje ya shigar bayan kammala zaɓen na watan Oktoban 2021, wata Kotun Tarayya ta ayyana ɓangaren Sanata Shekarau a matsayin waɗanda suka yi sahihin zaɓe kuma ta bayyana Ɗan-Zago a matsayin halastaccen shugaba. Kodayake ɓangaren gwamnan ya ɗaukaka ƙara.
A Jihar Kebbi ma haka lamarin yake, inda ɓangaren tsohon gwamna kuma sanata mai-ci, Muhammadu Adamu Aleiro, ya buɗe wata sabuwar hedikwatar jam’iyyar.
Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarensa da na gwamnan jihar, Sanata Atiku Bagudu da kwamitin Abdullahi Adamu ya yi.
Bangaren Gwamna Bagudu dai ya bayyana buɗe sabon ofishin a zaman haramtacce wanda aka yi ba bisa doka ba.