Connect with us

News

Buhari ya ƙaddamar da shirin rage haihuwa a Najeriya

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon tsari kan yawan jama’a don ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Advertisement

Shugaban ya ƙaddamar da wannan shiri ne a fadarsa da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Shugaban ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan ƙaruwar da ake samu na haihuwa ta hanyar faɗaɗa shirye-shiryen samar da hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani a faɗin ƙasar.

Domin tabbatar da wannan tsarin, shugaban ya kafa wani kwamiti da zai riƙa sa ido kan yawan jama’a wanda shi da kansa zai jagoranta, sai kuma mataimakinsa zai ci gaba da taimaka masa a wannan ɓangare haka kuma akwai shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnatin a matsayin mambobi.

Advertisement

Shugaba Buhari ya ce babban burin wannan shiri shi ne inganta rayuwar duka yan Najeriya wanda hakan na daga cikin abin da gwamnatin ƙasar ke son cimmawa.

Buhari ya ce ƴan Najeriya sun fi kowace al’umma yawa a nahiyar Afrika kuma ita ce ta bakwai a duniya baki ɗaya kuma tana daga cikin ƙasashe ƙalilan na duniya da ake ƙara samun haihuwa sosai – ƙasar ta dogara kan matasa inda sama da kashi 72 cikin 100 na matasan na ƙasa da shekara 30 inda rabin matan ƙasar na cikin shekarunsu na haihuwa wato tsakanin shekara 15 zuwa 49.

Ganin cewa kafin a ƙaddamar da wannan shiri akwai buƙatar samun sahihai da ingantattun bayanai kan adadin jama’a a Najeriya, Shugaba Buharin ya bayyana cewa bayanan da za a samu daga ƙidayar da za a yi a 2022 za ta samar da duka bayanan da ake buƙata domin aiwatar da shirin na tsarin iyali.

Advertisement

Shi ma shugaban hukumar ƙidayawa ta Najeriya Honarable Nasir Isa Kwarra ya buƙaci yan Najeriya su rungumi tsare-tsaren da gwamnatin ƙasar ta fitar kan batun haihuwa.

Honorable Isa Kwarra ya bayyana cewa an samar da wannan sabon shirin na gwamnatin tarayya ne bayan tuntuɓa daga masu ruwa da tsaki da kuma ƙungiyoyin da lamarin ya shafa a faɗin Najeriya.

Wani jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya Matthias Schmale, ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa wannan tsarin da Shugaba Buhari ya ƙaddamar zai yi nasara sakamakon dalilai da dama.

Advertisement

Hakazalika ya jinjina wa gwamnatin Najeriya kan ƙaddamar da shirin inda ya ce duniya baki ɗaya da Majalisar Ɗinkin Duniya na sa ran ganin Najeriya ta zama ƙasar da za a samu raguwa a fannin mutuwar ƙananan yara da raguwar samun ciki da ƙananan yara mata ke yi da haihuwa.

Haka kuma ya ce ana sa ran samun raguwa a yawan haihuwa baki ɗaya da ƙara rungumar hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *