Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta gano masu daukar nauyin Boko Haram 96

Published

on

FB IMG 16438990752182700
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Hukumar da ke tattara bayanan sirri kan kudade ta bankado masu samar da kudi dan ta’addamci 96 har da masu alaka da kamfanonin hada-hadar kudi 424.

Ministan yada lanarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ne a yau, yayin wani bayani da ya yi kan yaki da cin hanci da gwamnatin shugaba Buhari ke yi.

Advertisement

Ya kara da cewa an gano kamfanoni 123 da kamfanonin 33 na masu musayar kudi da ke da alaka da ‘yan ta’adda a Najeriya.

Ya ce, “A bangarenta, a sharhin da ta yi kan kudade na 2020-2021, ta bayyana masu hada-hadar kudade 96 da ke da alaka da ‘yan ta’adda a Najeriya, akwai kuma wasu 424 da ke samar da kudade domin ta’addanci da suka hadar da kamfanoni 123, da kuma na masu musayar kudi 33, bugu da kari an gano wasu 26 da ake zargi da ta’addanci da wasu 7 da ake hada kai da su kan harkokin ta’addanci. Wannan bayani ya kai ga kama 45 da ake zargi wadanda kwanan nan za a gabatar da su a gaban kotu.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *