News
Facebook: Masu amfani da shafin a kullum sun ragu karon farko cikin shekara 18
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Katafaren shafin sada zumunta da muhawara Facebook, ya samu raguwar masu amfani da shi a kullum (DAUs) karon farko a tarihinsa na shekara 18 da kafuwa.
Ainahin babban kamfanin Meta Networks, ya ce yawan masu amfani da shafin a kullum ya ragu zuwa 1.929bn a cikin wata uku zuwa karshen watan Disamba, idan aka kwatanta da da yawan da yake da shi na 1.930bn a watanni uku na baya.
Kamfanin ya kuma yi gargadin samun raguwar kudinsa saboda hamayya da yake fuskanta daga sauran shafuka irin su TikTok da YouTube, yayin da masu tallata kayansu a shafin suma suke rage kudin da suke kashewa.
Darajar hannun jarin kamfanin na Meta ta ragu da sama da kashi 20 cikin dari a cinikayyar ‘yan sa’o’i a kasuwar New York.
Faduwar darajar ta haifar da asarar kusan dala biliyan 200 (£147.5b
Haka kuma darajar hannun jarin sauran shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Twitter da Snap da Pinterest, ita ta fadi sosai a kasuwar.
Shugaban kamafanin na Facebook ya ce cinikin da kamfanin yake yi ya ragu saboda masu amfani da shafin musamman ma matasa sun koma wasu shafukan, abokan gogayyar facebook din.