News
Ranar Hijabi ta Duniya: Ɗalibai su na da ƴancin sanya hijabi a makarantu – Makinde

Daga kabiru basiru fulatan
Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo a ranar Talata ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa ba za ta take musu haƙƙinsu na addini ba.
Makinde ya baiyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin addinin musulunci, Abdulrasheed Abdazeez, ya fitar, domin bikin ranar Hijabi ta duniya ta 2022.
“Hijabi sutura ce da ba wai kawai tana kawata mai sakawa ba, har ma tana taimakawa wajen ci gaban ɗa’a a cikin al’umma,” inji Makinde.
Gwamnan ya taya al’ummar musulmin jihar murna musamman mata, ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa ba za ta soki duk wasu ɗabi’u da za su inganta ibada da kunya ba.
“Dalibai musulmi da suke son sanya hijabi a makarantun gwamnati a jihar Oyo ba a tauye musu hakkinsu ba,” in ji shi.
“Na umurci masu riƙe da muƙamai a ma’aikatan gwamnati da kuma ɗaukacin makarantun gwamnati da kada su tursasa kowa ko musgunawa wani saboda addininsa ko kuma ayyukansa.
“Gwamnatinmu mai tsoron Allah ce, kuma za mu ci gaba da wa’azin juriya na addini, daidaito da adalci, wanda zai kara samar da zaman lafiya da soyayya da hadin kai.
“Kamar yadda taken bikin na bana ya nuna, hijabi abin alfahari ne ga kowace mace musulma kuma ya kasance mai tsarki,” in ji shi.
Makinde ya kuma yi kira ga shuwagabannin addinai daban-daban da su rika hada kai da gwamnatin jihar kan kowane irin lamari domin kaucewa rikicin addini.