News
Zamfara: Ƴan Sanda sun tabbatar da yin garkuwa da mutum 4 da ga iyalin Shugaban ASUU
Daga yasir sani abdullahi
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da yin garkuwa da mutum 4 daga cikin iyalin Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU, da wani mutum ɗaya a jihar.
Rahotanni sun baiyana cewa ƴan bindigan sun kutsa kai gidan Shugaban ASUU, reshen Jamia’r Taraiya ta Zamfara, Abdulrahman Adamu, in da su ka yi awon-gaba da huɗu da ga cikin iyalinsa.
Da ya ke tabbatar da harin a jiya Laraba a Gusau, Kakakin Rundunar, Muhammed Shehu ya ce an zuba jami’an ƴan sanda na ɓangaren keƙen asiri domin su nemo waɗanda a ka yi garkuwa da su sannan su kuɓutar da su.
Shehu ya ƙara da cewa ƴan sanda na aiki da mahukuntan jami’ar domin samun bayanan sirri da kuma ɗaukar mataki na gaba.
Kamfanin Daillancin Labarai na ƙasa, NAN ya rawaito cewa ƴan bindigar sun dira a gidan shugaban ASUU ɗin da ke unguwar Damba da ke Gusau da tsakar dare, inda su ka fara harbin kan me uwa da wabi.
Wata majiya kusa da shugaban ta ce yan bindigar sun tafi da ƴaƴan ƴan uwan sa, namiji da mace, sannan su ka haɗa da kannen matar sa su biyu.
Haka-zalika an ce yan bindigar sun yi awon-gaba da wani ma’aikaci a sashen hada-hadar kuɗi na jami’ar, wanda a ka baiyana sunan da Alhaji Abbas.
NAN ta tuna cewa unguwar Damba ta sha fama da harin ƴan ta’adda a yankin, inda wannan harin ya zama shine na uku a cikin watanni biyu.