Sports
Ɗan wasan Faransa, Zouma na fuskantar shekara 4 a gidan yari sakamakon dukan kyanwarsa da ya yi
Daga Ibrahim abdullahi
Dan wasan kwallon kafar Faransa, na fuskantar daurin shekara 4 a gidan yarin Faransa idan har a ka kama shi da laifin da mari da kuma duka da kafa da ya yi was kyanwarsa a England.
Laifin, idan har ya tabbata, ya saɓawa sabuwar dokar kiyaye hakkin dabbobi ta Faransa.
Tun da fari dai an mika korafin ne a kan Zouma, dan wasan kungiyar kwallon kafa ta West Ham mai shekara 27 a birnin bayan da fefen bidiyo mai tada hankali yayin da a Ka nuna shi ya na dukan kyanwar ta sa a gidansa da ke unguwar Essex.
Hakan ne ya harzika lauyoyi da ke aiki a Gidauniyar Abokai Miliyan 30, gidauniya mafi girma da ke rajin kare hakkin dabbobi a Faransa su Ka shigar da kara.
“Mun yi alla-wadai da aika-aikar da Zouma ya yi. Mu na kira da a dakatar da shi a ƙungiyar ƙwallon ƙafar Faransa da kuma ta West Ham,” in ji kakakin ƙungiyar.
Kamar yadda sashe na 113-6 na kundin lefuka na ƙasar Faransa ya nuna cewa duk wani ɗan ƙasar ba zai tsallake hukunci ba ko da yya yi laifi a wata ƙasar.
Duk da cewa a 2021 a Ka ƙirƙiro da sabuwar dokar kare dabbobi, an tanadi hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yarin da kuma tara da ta kai kimanin fan ɗin England 50,000.
Daily Nigerian Hausa ta biyo cewa dubban ƴan Faransa ne su ke kira da a ɗaure Zouma bayan da su ka kalli wanna faifen bidiyo.