Sports
United ta barar da damar shiga jerin hudun farko na gasar Firimiya
Daga yasir sani abdullahi
Manchester United ta barar da damar shiga jerin kungiyoyi hudu na farko na gasar Firimiyar Ingila a ranar Talata, bayan da ta kasa doke Burnley a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1, abinda ya sanya a halin yanzu United din ke matsayi na 5 da maki 39.
Paul Pogba ne ya fara ci wa United kwallonta a minti na 18, yayin da Burnley ta rama ta hannun dan wasanta Rodriguez a minti na 47.
A karon farko tun bayan fara horas da United a Ralf Rangnick bai sanya Cristiano Ronaldo cikin tawagar kungiyar da ta fara wasa a matakin Lig na Firimiyar Ingila ba, matakin da ya sake bijiro da muhawarar cewa shin tawagar ‘yan wasan Manchester United ta fi karfi da kuma buga wasa mai kyau, ba tare da Ronaldo ba, ko kuma akasin haka.
A karshen makon jiya ne dai kungiyar Middlesbrough da ke matakin Championship na kasa da Firimiya ta fitar da United daga gasar cin kofin FA, wanda kuma a wasan ne Ronaldo ya gaza cin damar bugun daga kai sai mai tsaron raga da ya samu a cikin wasan.
Bayan karin lokaci ne kuma, Middlesbrough ta lallasa Manchester United da kwallaye 8 -7 a bugun fanareti.
Wasu dai na ganin da wuya Ronaldo ya ci gaba da zama a United saboda rashin karsashin kungiyar, yayin da tuni aka fara alakanta shi da komawa PSG, kungiyar da ake sa ran tsohon kocin Real Madrid Zidane zai karbi ragamar horas da ita daga Mauricio Pochhetino a karshen kakar wasa ta bana.