News
An naɗa sabon Kakakin Rundunar Ƴan Sanda na Ƙasa
Daga kabiru basiru fulatan
Sifeto-Janar na Ƴan Sanda na Ƙasa, Alkali Baba, ya naɗa Olumuyiwa Adejobi a matsayin sabon Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa.
Wani jam’i a Ofishin Hulɗa da Jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin shine ya sanar da naɗin a wata sanrwa a yau Asabar.
Ya ce naɗin na Adejobi ya zo ne bayan da a ka tura Frank Mba zuwa ƙaro karatu na Babban Jami’i a Cibiyar Horaswa a kan Ilimin Dabarun Mulki, NIPSS da ke Kuru a birnin Jos.
Adejobi, Chif Sifiritandan Ƴan Sanda ne, tsohon ɗalibin Jami’ar Ibadan ne, inda ya karanci fannin ‘ Archeology da Geography’ a haɗe.
Ya kuma yi digiri na biyu a fannin ilimin rikici da zaman lafiya a dai jami’ar ta Ibadan.