News
NDLEA ta cafke ɗan Indiya da kwalaben ‘codeine’ 134,700 da ya shigo da su Nijeriya
Daga kaniru basiru fulatan
Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, sun cafke wani ɗan ƙasar Indiya, Vyapak Nutal da kwalaben ‘codeine’134,700 da ya shigo da su cikin Nijeriya.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya sanya wa hannu a yau Lahadi, tuni dai Nutal na can ya na shan tuhuma.
A cewar Bababfemi, an kama ɗan Indiyan ne a tsakanin bidar Nijeriya da Nijar a Jihar Sokoto.
Ya ce ɗan Indiyan ya loda kayan ne a garin Kwatano a Ƙasar Jamhuriyar Benin zuwa bidar ta cikin jamhuriyar Nijar , yana shiga Sokoto, sai a ka cafke shi a Illela.
Ya ƙara da cewa an kama Nutal ne lokacin da ya ke kwance a wani otal a Sokoto.
Rahotannin sirri, in ji Bababfemi, sun nuna cewa dubun Nutal ta cika ne lokacin ya na tsaka da neman wanda zai sayi maganin tarin.
Daga bisani me, in ji sanarwar, sai Jami’an Ƴan Sandan Farin Kaya su ka kai sumame su ka cafke shi, sannan su ka damkawa jami’an NDLEA a ranar Laraba.