Connect with us

News

ASUU: Ni ɗan Najeriya ne mai bin doka da oda – Pantami

Published

on

FB IMG 1645108096418
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Ministan da yai kaurin suna wajen kuka, Isa Pantami, ya yi magana a karon farko bayan kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta ayyana shi a matsayin haramtaccen Farfesa.

Advertisement

Pantami wanda ya yi magana a ranar Laraba, yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala Taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaban Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ya ce ba zai ce komai ba, saboda taƙaddamar batun na kotu a gaban mai shari’a

“Na zo nan ne don in yi magana game da aikin da nake na ma’aikata ta”.

Sai dai kuma da aka tambaye shi game da cancantar sa na zama Farfesa, ya ki cewa komai.

“A matsayina na jami’in gwamnati, na san laifi ne in tsoma baki idan Kotu ba ta yanke hukunci ba. Kuma ni ‘dan Najeriya ne mai bin doka.” Inji Minstan

Advertisement

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin matsayar ASUU, wato Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, wadda ta ce digirin-digirgir ɗin Minista Pantami na ‘Jami’ar Jatau Na Albarkawa’ ne.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) sun yanke hukunci tare da ɗaukar matsayin cewa Digirin-digirgir na Farfesan da aka ba Ministan Sadarwar Zamani, Isa Pantami, haramtacce ne, don haka ba su yarda da shi ba.

Sun bayyana hakan ne bayan tashi daga taron su na tsawon kwanaki biyu da suka gudanar a Jami’ar Legas.

Majalisar Zartaswar ASUU ta ce ta bi diddigin yadda Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta bayar da muƙamin Farfesan Nazarin Kare Aikata Laifuka a Kafafen Sadarwar Zamani (Cyber security) cewa an kauce wa ƙa’ida da matakan da suka kamata ya bi kafin ya kai ga matsayin.

Advertisement

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, Emmanuel Osodeke, ya ce:

“Majalisar Zartaswar ASUU ta yi Allah-wadai da matsayin ‘Farfesan’ da aka bai wa Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami.

“Daga hujjojin da muka tattara kuma muka tabbatar, Dakta Pantami bai cancanci muƙamin Farfesa ba. Sannan kuma ba shi matsayin ya kauce wa tsari, matakai da ƙa’idojin da ya kamata ya bi kafin ya zama farfesa. Kuma kowa ko a wace jami’a ce, sai ya bi waɗannan hanyoyi da matakai sannan ya ke zama farfesa a jami’a.

“Majalisar Zartaswar ASUU na kira ga dukkan mambobin ta da sauran rassan ƙungiyar na faɗin ƙasar nan, kada su amince kuma kada su riƙa bai wa Pantami girman da ake bai wa Farfesa.”

Advertisement

ASUU ta ce matsayin da ta ɗauka a yanzu ƙarin jaddadawa ce kan matsayin ta na farko da ta ɗauka cikin 2021.

Daga nan ta ce dukkan mambobin ta da su ke da hannu wajen cuku-cukun bai wa Pantami matsayin farfesa, za a hukunta su, don na baya su ɗauki darasi.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *