News
IBTILA’I: Mata da yara 13 sun mutu bayan sun tsunduma rijiya a gidan biki

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wani jami’i a yau Alhamis yana sanar da cewa mata da yara mata sun 13 ne su ka rasu bayan da su ka tsunduma cikin rijiya gidan bikin aure a arewacin India.
Haɗarin ya faru ne a jiya Laraba a ƙauyen Nebua Narangia da ke gundumar Kushinagar a Jihar Uttar Pradesh.
Waɗanda su ka rasun, sun gamu da ajalinsu ne bayan da su ka tsaya a kan rufin rumfar da a ka yi wa rijiyar yayin da su ke kallon bikin haldi, ɗaya da ga cikin bukukuwan Hindu da a ke yi a ƙasar, inda a ke baɗawa ango da amarya wata hoda a yayin biki.
Nauyin mutane ne yasa sanya rufin ya rufta inda mutane 20 su ka afka cikin rijiyarrijiyar, in ji Kushinagar, Majistare ɗin S. Rajalingam.
Rahoton ya ce mutum 11 ne su ka rasu nan take inda a ka garzaya da 5 asibiti, a nan ne kuma 2 suma su ka rasu a asibitin.
Firaministan ƙasar, Narendra Modi ya baiyana alhininsa a kan ibtila’in, inda ya ce gwamnati za ta taimakawa waɗanda su ka ji raunuka da kuma iyalan waɗanda su ka rasu.