News
Pantami: Ku maida hankali kan Kwarewa fiye da samun takaradar Satifiket, Pantami ya shawarci Matasa.

Daga yasir sani abdullahi
Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya jaddada bukatar gwamnati a kowane matati da makarantu su fi maida hankali kwarewa fiye da samun takarardar shaida (Certificate).
Pantami yace hakan ba wai zai samar da ayyukan yi bane kaɗai, zai shawo kan matsalolin zaman kashe wando da kuma magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da su.
Channels tv tace Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron miƙa kyauta ga waɗan da suka samu nasara a gasar National Talent Hunt Challenge a jihar Katsina.
Bayan haka, Farfesa Pantami ya roki waɗan da suka shirya gasa su ɗauki bayanan mutanen da suka fafata domin samun saukin nemo su nan gaba.
A nasa ɓangaren, Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi bayani kan musabbabin shirya gasar da ya haɗa da ƙarin kwarin guiwa da gina kwarewar matasa a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Masari ya ce: “Wannan gasar zata kara ɗaga izzar jihar Katsina da kuma sanya jihar ta fita tsara daga cikin takwarorinta a ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya.”
An shirya gasar ne domin ɗaukar matakan da zasu zaƙulo yan takara masu kwarewa ba wai a jihar Katsina kaɗai ba, a ƙasa baki ɗaya.