Connect with us

News

Kayayyakin da Najeriya ke samarwa sun haɓaka da kashi 3.98 cikin 100

Published

on

Screenshot 20220218 105954
Spread the love

Daga aminu usman jibrin

Hukumar ƙididdiga a Najeriya National Bureau of Statistics (NBS) ta ce jumillar abin da Najeriya take samarwa da ake kira Gross Domestic Product (GDP) ya haɓaka da kashi 3.98 cikin 100 a wata ukun ƙarshe

na 2021.

Wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya Alhamis ya ce hakan na nuna cewa tattalin arzikin na kan hanyar da ta dace idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na 2020.

Advertisement

“GDP ya haɓaka da kashi 3.98 cikin 100 cikin wata uku na karshe na 2021, abin da ke nufin alamun samun ci gaba a wata uku masu zuwa tun bayan annobar korona a 2020 lokacin da samar da kayayyaki ya yi ƙasa da kashi 6.10 da kuma 3.62 a wata uku na biyu da na ukun 2020 sakamakon annobar,” a cewar rahoton.

Ya ƙara da cewa “haɓakar na nuna alamun ci gaba da warwarewar tattalin arziki, inda ya kai kashi 3.40 a 20221”.

Kazalika, sakamakon na wata ukun ƙarshe a 2021 ya zarta na 0.11 da aka samu a irin wannan lokaci na 2020, sannan ya yi ƙasa da wanda aka samu a wata uku na uku a 2021 (maki 0.05).

Advertisement

Rahoton ya ce jumillar kayayyakin da ‘yan Najeriya ke samarwa ya zuwa wata ukun na ƙarshe a 2021 ya kai triliyan 49 – N49,276,018.23.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *