News
Zulum ya gwangwaje tubabbun ƴan daba 152 da tallafin N100m
Daga kabiru basiru fulatan
A yau Juma’a dai wasu gungun matasa, su 152, waɗanda su ka yi adabo da dabanci, sun kasance baki har kunne, bayan da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya raba musu tallafin Naira Miliyan Ɗari, (N100 million) sakamakon tuba da su ka yi da daba.
Zulum, wanda ya raba tallafin a Maiduguri, bayan da waɗanda su ka amfana ɗin sun kammala horo a kan kasuwanci na tsawon wata ɗaya.
Ya ce an raba musu kuɗin ne domin su yi jari domin su dogara da kansu su kuma bada gudunmawa wajen ci gaban jihar.
A cewar sa, 16 da ga cikin matasan za su samu Naira Miliyan 2 kowannen su, bayan da sauran 136 kuma kowanne su zai karɓi Naira Dubu 500.
Zulum ya ƙara da cewa waɗanda su ka amfana ɗin za su biya rabin kuɗin da a ka basu a shekara uku.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa zai ɗauki nauyin karatun ɗa ɗaya da ga cikin ƴaƴan matasan kowannen su.
Ya ƙara da cewa sun kwashe shekaru da dama suna dabanci amma ba abinda su ka tsinana, inda ya ce in dai su ka rike wannan tallafin da zuciya ɗaya to za su samu ci gaba sosai a rayuwarsu.
-
News19 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
