News
An ci tarar tsohuwar Minista N4m bayan an same ta da laifin karɓar N450m da Diezani ta sace

Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC, reshen Jihar Gombe, a jiya ta samu hukunci a kan Sarah Ochekpe, tsohuwar Ministar Albarkatun Ruwa a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, da wasu mutane biyu, Evan Leo Sunday Jitong da kuma Raymond Dabo, wanda shi ne mataimakin darakta na yaƙin neman zaɓen Goodluck/Sambo 2015 kuma tsohon shugaban riko na jam’iyyar PDP na jihar Filato.
An yanke wa mutanen uku hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari ko su biya tarar N4m kowannen su a Babbar Kotu, ƙarƙashin Mai Shari’a H. M. Kurya a Jos, Jihar Filato.
A na yi musu wasu tuhume-tuhume uku da aka yi wa kwaskwarima, waɗanda su ka haɗa da haɗa baki da kuma karkatar da kuɗaɗe.
Ana zarginsu da karɓar kuɗi Naira miliyan 450 da ga bankin Fidelity Plc ta hanyar tsabar kudi da musayar waya daga wasu kamfanonin mai da tsohuwar Ministar Albarkatun Man fetur, Diezani Alison-Madueke, domin amfani da kuɗin wajen murɗa sakamakon zaɓen shugaban kasa na 2015.
Bincike ya nuna cewa a ranar 26 ga watan Maris, 2015, an cire kuɗi Naira miliyan 450 da ga Babban Bankin Nijeriya, CBN, ta bankin Fidelity Plc reshen Jos, inda aka miƙa wa waɗanda ake ƙara bayan sun sanya hannu don karbar kuɗin.
Duk da cewa wadanda a ke tuhumar sun yi ikirarin cewa sun mika kudin ne ga marigayi Sanata Gyang Pwajok, dan takarar gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2015, amma sun kasa bayar da gamsashshiyar shaida da ke tabbatar da ikirarin na su.