News
Kwankwaso ya ƙaddamar da ƙungiyar da ya kafa domin ceto Nijeriya da ga halin ƙaƙanikayi

Kwankwaso ya ƙaddamar da ƙungiyar da ya kafa domin ceto Nijeriya da ga halin ƙaƙanikayi
A jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya sanar da kafa wata ƙungiya a matsayin ‘Runduna ta Uku’ a Abuja.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa kafa ƙungiyar na da nasaba da wani yunƙuri na karɓar mulki da ga hannun jam’iyyar APC a 2023.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwankwaso, wanda shi ne ya shirya shi, ya ce burinsu na haɗa kai ne da ceto kasar nan.
“Dukkanmu mun bar gidajen mu domin halartar wannan taro. Rana ce ta musamman a rayuwar al’ummarmu. Rana ta musamman don ceto al’umma.
“Tun da daɗewa ƴan Nijeriya suna jiran wannan rana. Abokan ƴan Najeriya da ke waje sun daɗe su na jiran wannan rana kuma lokaci ya yi yau da kuma yanzu.
“A yau, duk al’ummar Nijeriya da ga ko wanne ɓangare da tushe ta taru a nan wajen. Ƙudirinmu ne na ganin mun ceto al’ummarmu daga wannan mawuyacin hali.
Kwankwaso ya ce ya gana da abokansa a lokacin kullen korona kuma ya yanke shawarar cewa dole ne a dauki matakin ceto Najeriya.
“Mun yanke shawarar cewa dole ne a fara samun Najeriya kafin siyasa. Yayin da wasu daga cikinmu za su so tsayawa takara, dole ne mu hada kai don ceto kasar.
“Kungiyar nan ta mu na da mambobi a kowace karamar hukuma da wajen kasar,” in ji Kwankwaso.