News
INEC ta sanar da ranakun da za a yi zaɓen 2023

Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Zaɓe ta Nijeriya, INEC ta fitar da jadawalin babban zaɓe na 2023, inda da sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya baiyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Asabar.
Kazalika, INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƴan majalisun tarayya tare da na shugaban ƙasar.
Sannan Yakubu ya ƙara da sanar da cewa za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.
A cewarsa, an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri’a.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen “a lokacin da ya dace”.