Sports
Inter Miami na zawarcin Messi, Haaland ya ƙi Madrid

Daga aminu usman jibrin
Kwantiragin ɗan wasan gaban Poland Robert Lewandowski zai ƙare a 2023, inda ɗan wasan mai shekara 33 ke son ƙulla sabuwar yarjejeniya da kulob din na ƙasar Jamus, babu dai wata tattaunawa da aka yi zuwa yanzu. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan gaban Borussia Dortmund kuma ɗan ƙasar Norway Erling Braut Haaland bai amince da komawa Real Madrid ba a ƙarshen kaka, kamar yadda tsohon ɗan wasan gaban Middlesbrough Jan Aage Fjortoft wanda shi ma ɗan Norway ne ya shaida. (Mundo Deportivo)
Barcelona na ta ƙara samun ci gaba a yunƙurinta na ɗaukar ɗan wasan gaban Ivory Coast Franck Kessie ba tare da biyan ko sisi ba a ƙarshen kaka idan kwantiragin ɗan wasan mai shekara 25 ta ƙare da AC Milan. (Sport – in Spanish)
Newcastle ta taushe hannu wajen ɗaukar ɗan wasan bayan Netherlands Sven Botman a watan Janairu kuma ɗan wasan mai shekara 22 wanda aka alaƙanta da Tottenham, ana sa ran zai koma AC Milan a ƙarshen kaka. (Todofichajes)
Andreas Christensen ya ce yana cikin wani hali a Chelsea ganin cewa kwantiraginsa da kulob din na daf da ƙarewa. (90 Min)
Ɗan wasan bayan Sporting Lisbon kuma ɗan ƙasar Portugal Goncalo Inacio ya amince ya saka hannu a sabon kwantiragi da kulob ɗin. Ɗan wasan mai shekara 20 ya ja hankalin Newcastle a watan Janairu. (Fabrizio Romano)
Real Sociedad da Atalanta na son ɗaukar ɗan wasan bayan Norwich City mai shekara 26 a matsayin ɗan wasan aro. (Norfolk Live)
Tsohon dan wasan tsakiyar Manchester United Roy Keane ya bai wa kulob ɗin shawarar cewa ta ɗauki kocin Athletico Madrid Diego Simeone a matsayin kocinta. (Goal)