News
NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol 649,300 da kuɗaɗe da ga Pakistan, Austria da Italiya a Legas
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Yaƙi da sha da Fataucin Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol mai nauyin miligiram 225 har guda 649,300 a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Jihar Legas.
A lokaci guda kuma NDLEA ɗin ta cafke wani ƙullin kuɗaɗen ƙasashen waje na ‘euro’ da adadin da ya kai ‘euro’ 809,850 da a ka shigo da su da ga Pakistan, Austria da Italiya a filin jirgin.
Jakin hukumar, Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
Babafemi ya yi bayanin cewa jami’an kamfanin Skyway Aviation Handling Company da ke kula da kayayyakin fasinjoji da jami’an sashin yaƙi da muggan kwayoyi ne su ka kama ƙwayar Tramadol din har guda 649,300 da a ka yi safarar sa da ga Pakistan ta Addis Ababa ta jirgin Ethiopia a ranar Laraba.
Ya ce an kama wani Nwadu Ekene Christian da a ke zargin shi ya shigo da kayan.