News
Fadin gaskiya ga masu mulki shine dalilin da yasa aka cire ni a matsayin gwamnan CBN – Sarki Sunusi
Daga Khadija adam abubakar
Muhammadu Sanusi II ya ce rashin bijirewa fadin gaskiya ga masu mulki ya sa aka cire shi daha rike mukamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da kuma sarkin birnin Kano.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wajen rufe taron AIG Public Leadership Programme na 2021, a Abuja, ranar Laraba.
A watan Afrilun shekarar 2014 ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tube Sanusi daga mukamin gwamnan babban bankin Najeriya CBN bisa ikirarin cewa wasu mutane a karkashin gwamnatinsa sun sace dala biliyan 49.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya sauke shi a matsayin Sarkin Kano a ranar 9 ga Maris, 2020.
“Na tsaya tsayin daka don fadin gaskiya ga mulki, dalilin da yasa aka cire ni a matsayin gwamnan CBN da kuma Sarkin Kano, amma hakan bai hana ni yin abin da nake ganin ya dace ba,” in ji Sanusi.
Ya koka da yadda ma’aikatan gwamnati suka yi amfani da lamirinsu don biyan bukatun kansu.
Ya kara da cewa, “A yau, za ka ga ma’aikatan gwamnati suna sace miliyoyi da biliyoyin Naira da ake son gina tituna, samar da wutar lantarki, ruwa, ilimi, abinci da sufuri, amma sai sh wawure wanda hakan zai cutar da mafi yawan ‘yan Najeriya.
Duk wadannan sun haifar da Boko Haram, makiyaya masu kisa, ‘yan fashi da kuma gwagwarmaya da makamai masu yawa, musamman a tsakanin matasa, wanda ya haifar da barazana mafi muni ga rayuwar bil’adama a duk fadin Najeriya.”