Connect with us

News

MURIC ta yabawa Rundunar Ƴan Sanda bisa amincewa da sanya hijabi ga ƴan sanda mata

Published

on

FB IMG 1646403326156
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Ƙungiyar Rajin Kare Ƴancin Musulmai ta Ƙasa, MURIC, ta yaba wa Sifeto-Janar na Ƴan Sanda, Usman Alƙali Baba a bisa amince wa da amfani da hijabi ga ƴan sanda mata a faɗin Nijeriya.

Shugaban MURIC, sashin Jihar Zamfara, Farfesa Ahmad Galadima, shi ya yi yabon a wata sanarwar sanya sanya wa hannu a yau Juma’a.

Kungiyar, a cikin sanarwar, ta baiyana cewa amincewar ta Sifeto-Janar wata babbar nasara ce.

Advertisement

MURIC ta ƙara da cewa wannan matakin na Sifeto-Janar zai ƙara martaba da darajar Rundunar Ƴan Sanda a idon al’umma.

Ƙungiyar ta godewa Rundunar Ƴan Sanda, musamman Sifeto-Janar, a bisa amincewa da amfani da hijabi ga ƴan sanda mata, bayan sauraron koken da Musulmai su ka yi.

Ta ƙara da cewa wannan amincewar ta sanya za a kalli Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa a matsayin wacce ta ke bin tsarin aikin ɗan sanda na duniya.

Advertisement

“Sabo da haka mu na baiwa masu baki da kunu shawara da su ɗauka cewa wannan matakin wani sabon salo ke a yaƙi da ƴancin ɗan adam,” in ji sanarwar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *