Connect with us

News

Pakistan: Mutane 30 sun rasu, 60 sun jikkata bayan da ɗan ƙunar baƙin-wake ya tada bam a masallaci

Published

on

FB IMG 1646403526476
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

 

Wasu ƴan ƙunar baƙin-wake sun tada bam a jikinsu a wani masallaci da ke Arewa-Maso-Yammacin Pakistan, inda mutane 30 su ka rasu nan take, wajen 60 kuma su ka ji raunuka, kamar yadda ƴan sanda da likitoci su ka baiyana.

Wani jami’in ƴan sanda, Haroon Raheed ya ce ƴan ta’addan sun kutsa kai cikin harabar masallacin da ke Peshawar, bayan da su ka bindige ƴan sandan da ke garin masallacin, kafin da ga bisani su tashi ban ɗin da ke jikin su.

Advertisement

 

Tuni dai a ka garzaya da gawawwakin da waɗanda su ka ji rauni zuwa asibitin Lady Reading, wanda shi ne babban asibiti a garin.

Hukumomin na hasashen yawan mamatan zai ƙaru bayan da dama da ga cikin waɗanda su ka ji raunuka su na cikin halin rai-kokai mutu-kokai.

Advertisement

 

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *