Rukuni na biyu na ‘yan Najeriya ya isa Abuja daga ƙasar Hungary bayan sun tsallaka ƙasar daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake tafkawa a can.
Mutanen waɗanda mafi yawansu ɗalibai ne, sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da misalin ƙarfe 11:50 na daren ranar 4 ga watan Maris, a cewar hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.
Najeriya ta ce tana yunƙurin kwaso ‘yan ƙasarta kusan 5,000 daga ƙasashe maƙotan Ukraine, inda za a kashe aƙalla naira biliyan uku da rabi.