Connect with us

News

Wasu masu son zama shugaban ƙasa ya kamata a ce suna gidan yari – Obasanjo

Published

on

Screenshot 20220305 184154
Spread the love

Daga mujahid danllami garba

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce wasu masu burin zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya kamata a ce suna gidan yari idan da hukumomin da ke yaƙi da rashawa a Najeriya suna aikinsu yadda ya dace.

Tsohon shugaban ya faɗi haka ne a wani babban taron ƙara wa juna sani da aka gudanar a Abeokuta jihar Ogun domin bikin cikarsa shekara 85 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

“Na kalli wasu daga cikin mutanen da ke yawo da kuma wadanda mutane ke yawo da su. Idan da EFCC da ICPC za su yi aikinsu yadda ya kamata da kuma goyon bayan ɓangaren shari’a, da yawancinsu suna gidan yari.”

Advertisement

Duk wanda da ba ya da gaskiya a ƙananan abubuwa ba zai iya gaskiya ba manyan abubuwa,” in ji Obasanjo.

Tsohon shugaban na Najeriya ya kuma ce babu wani ɗan takara a yanzu da yake goyon baya, duk da ya ce wasu daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa sun kai masa ziyara suna neman goyon bayansa.

Obasanjo ya kuma ƙaryata rahotannin da suka lissafa wasu ƴan takara a yankin kudu da yake marawa baya.

Advertisement

“A irin wannan hali da muke ciki, ba zan yi gaggawar faɗin sunaye, ba tare da tuntuɓa ba da kuma tabbatar da ingantattun ka’idoji da matakai ba,” in ji shi.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *