Sports
Yakin Ukraine: Ɗaliban Najeriya na biyan sama da dala 1,000 domin fita daga Ukraine’
Daga mujahid danllami garba
Wani bidiyo da ya ɓulla a shafukan zumunta ya nuna dandazon ɗaliban na ife-ifen neman taimako, suna cewa “we want to go home” – “muna so mu koma gida”
Matasan waɗanda suka ce ɗalibai ne a Jami’ar Sumy, sun ce yanzu haka ba su da ruwan sha, ba wuta sannan abincinsu ya kusa ƙarewa.
“Yanzu mun kwana kusan uku ba mu yi wanka ba,” in ji wata ɗaliba da ta yi magana a bidiyon.
Wannan koken na su na zuwa ne adaidai lokacin da hukumomin Najeriya sun suka ce sun fara tattaunawa da wasu ƙasashen Turai don ganin ‘yan ƙasar su ci gaba da karatu a can, bayan tserewa yaƙi a Ukraine.
A wani ɓangaren kuma ɗaliban da suka dawo gida da BBC ta tuntuɓa sun shaida mata yada abokansu da suka saura a Ukraine ake cewa su bada sama da dala dubu kafin su fice zuwa kasashe makwabta.
Bayanan gwamnatin Najeriya
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce hukumomin Romania sun bai wa daliban kasar damar ci gaba da karatu a jami’o’in kasar, bayan sun tsere daga Ukraine sakamakon yakin da ake tafkawa a kasar.
Babban sakatare a ma’aikatar, Gabriel Aduda, ya ce suna kan tattaunawa da ministan ilimi na Romania domin karbar daliban Najeriyar.
Mista Aduda ya kara da cewa yanzu haka suna tattaunawa da sauran makwaftan kasashe kamar Poland da Hungary da Girka da Slovakia da Luthuenia don su bai wa ‘yan Najeriya irin wannan damar ta ci gaba da karatunsu.
Sai dai duk da haka, Najeriya ta ci gaba da aikin kwaso ‘yan ƙasarta daga ƙasashe makwabtan Ukraine, kafin kammala tattaunawa tsakanin hukumomin ƙasashen ta yadda za su iya komawa ƙetare don su ci gaba da karatu.
Martanin ɗalibai
Tuni daliban da suke can Ukraine da wadanda suka samu dawowa gida suka fara maida martani akan wannan dama da wasu kasashen suka fara bai wa daliban Najeriyar.
Daya daga cikin su da ba ta so a bayyana sunan ta ba, ta shaidawa BBC cewa; ”Ina son a taimaka a bari mu kammala karatunmu a can saboda yawanci mun yi nisa, wasu shekarar karshe suke wasu sauran shekara Daya ta rage su kammala karatu.
Kuma yanzu idan muka ce za mu dawo Najeriya baya za a maida mu, indai za a taimaka mana an yi mana adalci mu na son karasawa a can.”
Shi ma wani dalibin da ya gujewa yakin zuwa Poland daga Ukraine, yayi fatan za a sami saukin biyan kudi tare da jajircewa a tabbatar da kudirin ya kai gaci don kar karatun da suka fara ya shiririce.
“Yawanci mun zo Ukraine saboda karatun da sauki, idan kasashen za su dauke mu da ragin kudin makaranta ko ma kyauta, za mu so hakan.
“Duk da hakan mun godewa hukumomi da gwamnatin Najeriya da suka dawo da mu gida.
“Amma har yanzu akwai abokan mu dalibai a Sumy, su na cikin halin tashin hankali, sai sun biya sama da dala dubu ake fito da su, dan allah gwamnati ta taimaka ta fitar da su. Dalibai sun fi 1500 a can dan Allah a taimaka a kubutar da su.”
Tuni aka kwaso ‘yan Najeriya kusan 1,000 amma har yanzu akwai dalibai da dama a yankin Sumy na Ukraine da ke neman tallafin gwamnatin Najeriya don su koma gida ko kuma wata kasa mai aminci.
Sai dai duk da wannan sabon yunkuri na baiwa daliban Najeriya wuraren da za su ci gaba da karatunsu, mai yiwuwa sai an kammala mayar da su gida ne sannan tsarin komawarsu karatun a kasashe irin su Romania da sauran kasashen zai kankama.
