News
Ƴan Sanda sun cafke ɗan sandan boge da ke damfarar al’umma a Kano

Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Yusuf Abdullahi, wanda ya yi wa kansa laƙabi da Abdullahi Sarari bisa zargin damfarar al’umma ta hanyar amfani da kakin ƴan sanda ya karɓe kayan mutane.
Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwar sanya fitar a yau Talata, ya ce wanda a ke zargin ya karɓe wa mutane 3 kaya na kimanin Naira dubu 104 kuma bai tura musu kuɗin ta banki ba.
A cewar Kiyawa, rundunar ta samu rahoton wanda a ke zargi ne bayan da wasu ƴan kasuwa uku su kai ƙara cewa ya karɓe musu kaya kuma yayi alkawarin aika musu kuɗin ta banki amma har yau ba su ga alamar aiko kuɗin ba.
Sun ƙara da cewa sun amince wa Abdullahi ne sabo da sun gan shi da kakin ƴan sanda, amma sun ta buga wayar da bai daga ba.
Koyawa ya ce bayan da rundunar ta samu labarin, sai Kwamishinan Ƴan Sanda ya bada umarnin a nemo wanda a ke zargi, inda bayan ɗan wani lokaci, tuni a ka cafke shi.
A cewar Kiyawa, a jawabin da wanda ake zargin ya bayar, ya ce ya dade yana don shiga aikin ɗan sanda bai samu ba, shine yanke wajen taka ya dinka masa jakin ƴan sanda ya riƙa saka wa yana damfarar jama’a.
Koyawa ya ce rundunar ta fara bincike kuma za ta gurfanar da Abdullahi ɗin a gaban kotu, inda ya yi gargaɗi ga masu aikata laifi da su sake tunani domin rundunar ba za ta saurara wa kowa ba.