Connect with us

News

Ana ci gaba da zaman makoki bayan hallaka wasu ‘yan mata yaya da ƙanwa lokacin da suke tsakiyar cin kasuwa a garin Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa a jihar Kaduna arewacin Najeriya.

Published

on

Spread the love

 

Bayanai sun nuna cewa yankin karamar hukumar Giwa da ke makwabtaka da Birnin Gwari na fama da matsaloli na hare-haren ‘yan fashin daji.

Wani mazaunin yankin Kidandan ya shaida wa BBC cewa ‘yan matan biyu sun gamu da ajalinsu ne bayan da wasu jami’an tsaro suka yi dirar mikiya tare da bude wuta lokacin ana tsaka da cin kasuwa a ranar Alhamis.

Advertisement

Ya kuma kara da cewa: “Sojojin Dogon Dawa ne suka dira cikin motoci biyu a cikin kasuwar daidai wurin ‘yan awo.”

Kasuwar ta hargitse a lokacin da muka ji karar harbi a wajen cincirindon Fulanin da suka je cin kasuwa, muna tunanin ƙila sojojin sun je ne don farautar masu laifi, amma kuma sai suka bude wuta kan mai uwa da wabi,” ya ce.

Wasu hotuna da aka aiko wa BBC sun nuna gawawwakin ‘yan mata biyu kafin a yi musu jana’iza dauke da raunukan da suka yi kama da na harashi a gangar jiki.

Advertisement

Wani yayan ‘yan matan ya bayyana wa BBC yanayin yadda aka harbi ƙannen nasa.

“Daya harbin an yi shi a ƙirji ne ya fita ta baya, ɗaya kuma an yi shi ne a kafaɗarta har ya fito ya taɓa mamanta, sun zo su yi sayayya a kasuwa ne wannan abu ya same su” in ji yayansu.

“Da farko daya daga cikin sojojin na cikin motar a-kori-kura ta Hilux din ya fito ya ga yarinyar a kwance, sai kuma ya yi gaba ya kara ganin wata sai ya ce mutane su zo su dauke ta su kawo motarsu, amma kafin a kawo su sun hau motarsu sun wuce.”

Advertisement

Malamin ya kuma kara da cewa nan take dayar da mutu a yayin da kuma dayar ta rasu ana zuwa asibiti.

“Motocin sojojin guda biyu ne, akwai wacce harsashi ba ya tabawa sai kuma akori-kura kirar Hilux.”

Nurul Huda da Khadija

Ita dai Nurul Huda mai shekara 15 da kanwarta Khadija mai shekara 13 ba su jima da tasowa daga makarantar sakandaren da suke zuwa ba a ranar da lamarin ya faru.

Advertisement

Mahaifiyarsu Marwanatu Dayyabu ta shaida wa BBC cewa ta aike su kasuwa ne don sayo mata lalle, ba tare da masaniyar cewa ganin karshe kenan da ta yi wa ‘ya’yan nata a raye.

Ta kuma ƙara da cewa tana tsakar gida ina aikace-aikace lokacin da na ji harbin bindiga sau biyu, amma ba ta san cewa ashe a kan ‘ya’yanta ba harbin ya fada ba.

“Ina girki na sunkuya haka zan iza wuta sai na ji kara tas! Sai na kara jin tas! Sai na mike, da na miƙe sai na ce kai wannan ƙarar bindiga da muka ji, ta Fulani ce ko kuma ta sojoji? Sai suka ce ai harbin masu dawa ne,” in ji Marwanatu.

Advertisement

Marwanatu dai ta ce daman kunnuwansu sun saba jin karar harbe-harbe kasancewa yanki ne da aka dade ana fama da hare-haren ‘yan fashin daji da kuma artabunsu da jami’an tsaro.

Daga bisani ne in ji Marwanatu yayansu ya rugo da gudu ya fada mata faruwar al’amarin.

“Da ya zo sai ya fada min cewa ita karamar an kai ta asibiti, babbar kuma an taho da ita gida, to karamar dai ta dai bude ido lokacin da aka kai ta asibiti sai ta yi salati sau uku.

Advertisement

“Daga nan tun da idanunta suka rube shikenan tafiyar kenan, sai aka kwaso ta aka kawao cikin dakin babanta,” ta bayyana.

Shi ma a hirarsa da BBC mahaifin ‘yan matan Malam Dayyabu Iyal ya yi kira ga hukumomi da su gudanar da bincike don bi masa kadin abinda ya kira kisan ‘yayansa mata da ba su ji ba ba su gani ba.

“Yanzu mu dai tun da talakawa ne, halin da ake ciki shine muna rokon gwamnati da ta bincike wadannan abubuwa,” in ji shi.

Advertisement

Wani mazaunin Kidandan din ya kara jaddada wa BBC cewa irin wannan matsala ta harbin kan mai uwa da wabi a kasuwannin yankin abu ne da ya zama ruwan dare.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da kai hare-hare da satar mutane don neman kudin fansa ke karuwa, lamarin da a cewarsa ya zame musu tamkar rana zafi inuwa ƙuna.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *