News
Rikicin APC: Ni ban karɓi wata wasiƙa da ga Buni ba — Sani Bello
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shugaban riƙo, na Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC, Abubakar Sani Bello, ya musanta karɓar wasiƙa da ga Shugaban kwamitin da ke cikin rikici, Gwamna Mai Mala Buni.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa rahotanni sun baiyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin a tsige Buni da ga shugabancin kwamitin riƙo na APC saboda zargin wargatsa shirin da a ka yi na yin babban taron jam’iyar a ranar 26 ga Maris.
Sai dai kuma wata wasika da aka ce Buni ne ya rubuta ta har ya na baiwa Gwamnan Jihar Naija umarnin ya karɓi rikon jam’iyar na wucin-gadi an gan ta tana ta yawo a kafafen sadarwa.
Sai dai kuma dan a ke ganawa da manema labarai a yau Alhamis bayan wata ganawa ta kwamitin rikon, Sani Bello ya ce bai samu wasikar ba.
Ya ce shi dai abin da ya sani shine jam’iyar ta aike wa da Hukumar Zaɓe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC inda ta baiyana shirinta na yin babban taron ta a ranar 26 ga watan Maris.
