Connect with us

News

Gwamnatin Kano ta ja kunnen malaman addini da ‘yan Tiktok ‘kan wa’azin Daurawa

Published

on

Advertisements
ads

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi wa Malaman addinin Musulunci gargadi da masu amfani da shafukan sada zumunta da su lura da abin da suke faɗa domin harshe ka iya kai su ya baro su.

Cikin wani hoton bidiyo na minti biyar da kwamishinan addinai na jihar Muhammad Tahar Adam Baba Impossible ya yi, ya bayyana matsayar gwamnatin Jihar Kano kan ce-ce-ku-cen da ya ɓarke bayan yaɗuwar wani bidiyo da Sheikh Daurawa ke magana a kan al’aurar mata da kuma martanin da Nafisa Ishak wata mai amfani da shafin Tiktok ta yi.

A makon da ya gabata ne Sheikh Daurawa a wani bidiyo aka ji yana ba da misali da yadda al’aurar mata ke da muni duk da cewa yana cikin ƙwace-ƙawacen duniya.

Hakan ya sa mutane suka yi ta mayar da martani daga ɓangarori daban-daban, sai dai mafi jan hankali shi ne na wata mai amfani da shafin Tiktok Nafisa wacce ta yi “kakkausan martani” ga Malam Daurawan.

Daga baya kuma wani malamin mai suna Asadus Sunnah ya yi nasa bidiyon yana gargaɗin Nafisan tare da yin barazanar cewa suna da yaran da za su tura su yi maganinta.

Advertisement

Kwamishinan addinan ya cewa BBC abin da ya sa gwamnati ba ta yi magana tun da farkon lamarin ba, saboda ta tsaya tattara bayanai ne daga ɓangarorin kafin yanke hukunci.

Baba Impossible ya fara da bayani ne kan cewa Malam Daurawa bai yi dai-dai ba kan bayanan da ya yi, yayin wani karatu a ranar Litinin wanda yake yi kullum.

Gwamnatin jihar Kano ta ji ta kuma saurari abubuwan da ke faruwa duka, ta tambayi malamai da masana, an kuma ji bangarori daban-daban kuma an kalli jawabin kowa.

“Abin da ma’aikata ta tsaya a kansa, kamar yadda muka ji daga bakin malamai, shi mai jawabi na farko ya yi kuskure a jawabinsa, kamata ya yi ya tsaya kan Ƙala Allahu ƙala Rasulihi.

“Idan akwai wani ƙarin bayani kar a yi shi cikin yadda zai yamutsa hazo yadda zai ta da ƙura, yadda zai tayar da hankalin mutane yadda zai zama kamar akwai batsa, kamar akwai cin mutunci, kamata ya yi a saya shi.

“Don haka tun a nan muka fuskanci akwai kuskure a jawabin da ya yi,” in ji Baba Impossible.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa malami ba ma’asumi ba ne zai iya yin kuskure, don haka idan malami ya yi kuskure ya iya gyarawa.

Cikin bayanansa ya riƙa kin ambatar sunan Malam Aminu Daurawa, inda ya riƙa siffanta shi da mai magana na farko ko kuma mai wa’azi.

Da yake bayani a kan Nafisa Ishak, Kwamishinan ya ce ita ma a jawabanta akwai kuskure masu yawa kuma sun yi nazari kansu.

“Ba ta cikin rukunin wadanda za su iya mayar wa da Malamin martani, idan malami ya yi maganar malami dan uwansa ya kamata ya mayar masa da martani idan da kuskure ya fada masa cewa bai yi dai-dai ba ya gyara.

“Amma ba ita da take matar wani ko budurwa ko bazawara ba.

“Maganganun da ta yi sun yi tsauri, don haka ba mu yarda da abin da ta fada ba, ba dai-dai ba ne, ko da yake dai ba zagi ba ne kai tsaye, amma zagi ne idan aka kalli yadda ta furta su,” in ji Kwamishinan addinan.

Advertisement

Gwamnati ba za ta yarda da daukar doka a hannu ba’

Muhammad Tahar ta cikin wannan bidiyon ya bayyana cewa ba wani abu ba ne ya fi tayar wa da Gwamnatin Kano hankali ba, fa ce kalaman malaman addini.

“Jawabai da muka ji daga wasu Malami a kan mimbarin masallaci ko a makaranta, wani Malami an ji shi yana cewa, suna da matasa suna da ‘yan daba wadanda za su iya turawa.

“Idan sun ce a yi wa mutum duka a yi masa in sun ce a kashe mutum, a kashe mutum, wannan babban lamari ne wanda gwamnati ba za ta zuba ido a kansa ba.

“Sannan a cikin jawaban da aka riƙa zagin wannan yarinya da mayar da martani wadansu suna cewa za su sace ta wasu na cewa za su yi mata fyade wasu na cewa za su kashe ta, to wannan abin ya tayar da hankalin gwamnati,” a cewar kwamishinan.

Ya ce kowa ya sani cewa jami’an tsaro na kallo tare da bibiyar wadannan mutanen da suka riƙa yi wa wannan yarinya barazana.

Kuma matsayar Gwamnati kan wannan bincike da ta yi shi ne ba za ta yarda da dabanci ba, ba za ta yarda da ɗaukar doka a hannu ba, ba za ta yarda da don an ɓata wani wani ya fito ya rama ba.

Advertisement

Abin da yake a doka in ji Kwamishinan shi ne duk wanda aka taɓa nasa kuma yake ganin ba zai hakura ba sai ya tafi kotu.

Ya ƙara da cewa ‘yan sanda za su bincika su gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu kuma kutu ta yi masa hukunci.

Muna kira ga su malamai su san abin da suke furtawa kuma su iya bakinsu, su rika furta abin da zai amfani jama’a, in ji Baba Impossible.

Ra’ayin malami kana da ikon kayar da da shi ko kar ka yarda da shi.

“Ba za mu yarda a ci mutunci Malami ba ko ma wanda ba malami ba domin duka a ƙasanmu suke”.

Asalin turka-turkar

Wannan turka-turka ta samo asali ne cikin wani karatu da Malam Aminu Daurawa ya yi wanda yake lissafa abubuwan da su ne jin dadin duniya a wajen dan adam, sai dai a wajen Ubangijinsa ba komai ba ne.

Advertisement

Ya ambato abubuwa guda biyar waɗanda ba ma masu burgewa ba ne, irinsu tufafin alhariri da kashin ƙudan zuma, har ya zo kan batun mace.

Ya ce “Idan ka ce mace ce daɗin duniya mece ce macen? Mafi muni a jikin mace shi ne gabanta, ta nan take fitsari nan take fitar da jini, to meye na birgewa”.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending