Connect with us

Sports

Paul Pogba: Barayi sun shiga gidan Pogba lokacin yana wasa da Atletico Madrid

Published

on

Muslim yunus Abdullahi

Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba ya ce barayi sun shiga gidansa lokacin da yake buga wasan Champions tsakaninsu da Atletico Madrid a ranar Talata.

Advertisement

An saka dan kwallon Faransa a cikin wasan ne lokacin ana minti 67 da soma wa kuma an shiga gaban United da ci daya.

Pogba yace “Abin da ya fi tsoratar da um shi ne fasa gidanmu lokacin ‘ya’yanmu na bacci a dakinsu”.

Advertisement

Mai hidiga a gidan tana nan lokacin da lamarin ya faru kuma Pogba ya ce zai bayar da tukwici ga “duk wanda ya taimaka wajen gano mutanen”.

Pogba na da yara biyu ‘yan shekaru uku da ɗaya.

Advertisement

Dan wasan mai shekaru 29 ya sake koma Old Trafford ne a shekara ta 2016 daga Juventus a kan fan miliyan 89.

A karshen kakar wasan bana kwangilarsa za ta kare a United.

Advertisement

“Da ni da matata muka yi sauri muka koma gida sai muka tarar da babu abin da ya samu ‘ya’yanmu,” in ji Pogba.

Dan kwallon Manchester City Joao Cancelo ya ji rauni lokacin da ‘yan daba suka nemi kutsawa gidansa lokacin bikin kirismeti.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending