Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Haaland, Conte, Messi, Tuchel, Lewandowski, Origi, Haller
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Barcelona ta bayyana sha’awarta ta sayen Marcus Rashford. A shekara ta 2019 Rashford ya amince da kwantiragin karbar albashin fam 200,000 a duk sati a Manchester United har zuwa watan Yuni
Cristiano Ronaldo, na shirin ci gaba da zama a Manchester United a kaka ta gaba inda shi kuma mai horas da kungiyar na wucin-gadi Ralf Rangnick ake ganin watakila ya tafi. (AS)
Arsenal ta zaku ta sayi tsohon dan wasan Chelsea na Real Madrid a yanzu Eden Hazard. Dan wasan gaban na Belgium, mai shekara 31 ya koma Real ne a 2019. (FootMercato – in French)
Benfica ta sanya farashin fam miliyan 67 a kan dan wasanta na gaba dan Uruguay Darwin Nunez, mai shekara22, wanda ya taimaka wa kungiyar tasa ta Portugal ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai. Kungiyoyin da suka hada da Arsenal da Manchester United da Newcastle na sha’awar Nunez. (Mirror)
Watakila Manchester United ta nemi sayen matashin dan wasan tsakiya na Ajax da tawagar Holland Ryan Gravenberch. (The Athletic – subscription required)

Ga alama ba lalle ba ne ‘yan wasan da Chelsea ke neman saye, su samu zuwa kungiyar mai rike da kofin Zakarun Turai a bazaran nan, kamar yadda wani wakili ya yi gargadi.
Rahotanni na danganta kungiyar da ‘yan wasan da suka hada da Declan Rice, na West Ham, dan Ingila mai shekara 23. (Daily Mail)
Wakilin Jorginho ya ce abin da dan wasan dan Italiya ya fi so a yanzu shi ne ya kulla sabuwar yarjejeniya da Chelsea, duk da sha’awarsa da taurarin Serie A, Juventus ke yi. (90 Min)
Antonio Conte ba zai bar Tottenham ba a bazaran nan in ji kyaftin din kungiyar Hugo Lloris. Golan na Faransa mai shekara 35 na ganin kocin dan Italiya ba irin wanda zai gajiya ba ne a kowa ne irin hali. (Evening Standard)
Dan gaban Liverpool dan Belgium Divock Origi, mai shekara 26, zai koma AC Milan a bazaran nan. (Fabrizio Romano)

Ta daya a gasar Championship, Fulham na shirin sayen ‘yan bayan Liverpool Joe Gomez da Neco Williams. Liverpool ta yi kiyasin Gomez, dan wasan Ingila mai shekara 24, zai kai farashin fam miliyan 23. Shi kuwa
Williams, dan bayan Wales mai shekara 20, a yanzu yana zaman aro a Fulham. (Express)
