Interview
Komawar Matasa Harkar Noma Da Kiwo Itace Hanyar Da Zata Kawo Cigaba A Najeriya-“Ahmad Ahmad Alkasim”
Daga maryam bashir musa
Komawar matasa harkar noma da kiwo hanya ce wace zata kawo babban sauyi a kasa baki daya,duba da yanayi da matasan kasar ke ciki na rashin aikin yi, yabaiyana hakan ne a yayin tattaunawar sa da wakilin mu kabiru basiru fulatan.
Yana mai cewa matasa yakamata su maida hankali a akan harkar noma da kiwo dan samarwa kansu aikin yi da ciyar da kasa baki daya dan yakamata matasa su daina la’akari da aikin gwamnati, yakamata suyi tunanin hanyar yanda zasu dogara da kansu.
Dan haka ina mai bawa matasa shawara akan su zo tarun da kungiyar ALL FARMARS ASSOCIATION OF NIGRRIAN (AFAN) ta shirya kamar haka;- 24/03/2022 wanda za,ayi a MUMBIYYA HOUSE da misalin karfe 10:00am Na Safe inda za’a wayarwa matasa kai akan harkokin noma na zamani.
Ahmad ahmad alkasim yara da cewa yakamata matasa sumai da hankali wajan samarwa kansu mafuta ta hanyar noma da kiwo dan ciyar da kasa baki daya
