Connect with us

News

2023: Atiku zai sanar da takarar shi a hukumance a ranar Laraba

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

 

A ranar Laraba ne dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar zai sanar da takarar shi ta shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa na 2023.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa Atiku zai sanar da takarar ta shi ne bayan ya ɗauki watanni ya na tuntubar masu ruwa da tsaki a ciki da wajen ƙasar nan.

A wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Atiku ya fitar a Abuja, za a yi taron ne a International Conference Centre da misalin ƙarfe 11 na safe, inda a ke tsammanin ƴan ‘uwa, abokan gwagwarmaya, jagororin siyasa, ƴan jam’iya da kuma magoya bayan Atiku za su halarta.

Sanarwar ta ce taron shine aza tubalin shiga yaƙin neman zaɓen Atiku ɗin a ƙarƙashin jam’iyar adawa ta PDP.

A makon da ya gabata ne dai Atiku ya baiyana cewa wata kungiyar ƴan kasuwa ta Arewa ta sai masa fom ɗin takara.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending