News
An ci tarar wani mai mota saboda tuƙin ganganci da ya yi da budurwarsa
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wata kotu a Kenya ta ci tarar wani mai mota bayan da ta same shi da laifin tuƙin ganganci a kan wata babbar hanya yayin da wata fasinja a cikin motar ke ihu da karfi kuma ɗaya daga cikin ƙofofin motar na buɗe.
An yaɗa hotunan abin da ya faru a shafukan sada zumunta:
Ƴan sandan Kenya sun ce matar da ke cikin motar budurwar mai motar ce, wadda ta so ya sauke ta daga motar amma ya ƙi, kuma ya nace sai ta bi shi gidansa domin su ɗan shaƙata.
Sai dai sun ce mutumin da matar sun so su janye batun daga hannun ƴan sanda bayan da suka sasanta tsakaninsu.
Amma ƴan sanda ba su amince da wannan matakin ba, domin sun tuhumi mutumin da tuƙin ganganci da kuma saka rayuwar matar da sauran masu amfani da hanyar cikin haɗari.
Mutumin mai suna James Maina Kibe ya amsa laifinsa kuma kotu ta ci shi tarar kimanin dalar Amurka 600 baya ga dakatar da lasisinsa na tuƙi na wani lokaci.
