Connect with us

News

Najeriya ta soke yin gwajin korona ga matafiyan da suke son shiga ko ficewa daga ƙasar

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Advertisements
Advertisements

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa dukkan matafiyan da aka yi wa cikakkun alluran riga-kafin korona ba sa bukatar yin gwajin cutar na PCR COVID-19.

Wannan ne matakin farko da kasar ta ɗauka kan wannan batun na kiwon lafiya tun da ta fara ganin raguwar alƙaluman masu kamuwa da cutar.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke sa ido kan yaƙi da annobar korona a Najeriya, Boss Mustapha ya sanar cewa daga ranar 4 ga watan Afrilu wannan matakin zai fara aiki.

Advertisements

Sai dai ya bayyana cewa dukkan fasinjojin da ba a yi wa alluran riga-kafi ba, ko ma waɗanda ba a yi musu cikakkun alluran korona ba, tilas su yi wannnan gwajin akalla sa’a 48 kafin su bar ƙasar, ko kuma su yi gwaji na rana ta biyu ko rana ta 7 bayan sun isa ƙasar.

Advertisements
Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending