News
Ƴan sandan Najeriya sun kama matar da ta ƙona ƴarta ƴar shekara 10
Daga Yasir sani abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wata mahaifiya mai ‘ya’ya biyar bisa zargin ƙona ‘yarta ‘yar shekara goma.
An kama matar ne bayan wani mutum ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Mowe, yana cewa matar wadda suke zaune gida ɗaya da ita, ta zazzaga wa yarinyar fetur sannan ta banka wuta.
A cewar mutumin da ya shigar da ƙorafi wajen ‘ya sanda, Moroof Ayinde, matar ta ƙona ‘yar tane bayan ta zarge ta da daukar mata wayar salula bayan ta karɓa daga hannun ɗaya daga cikin ƙannenta.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya fada wa manema labarai a Abeokuta cewa bayan samun rahoton abin da ya faru, ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kama matar.
Abimbola Oyeyemi ya ce ‘yar, ta samu mummunar ƙuna a jiki, abin ya sa aka garzaya da ita asibiti mafi kusa kafin daga bisani a mayar da ita zuwa asibitin koyarwa na Olabisi Onabanjo domin samun kyakkyawar kulawa.
‘Yan sanda sun ce daga binciken farko-farko da suka gudanar, mahaifiyar da ake zargi wadda ta yi iƙirarin cewa sun rabu da mahaifin yaran, ta fada musu cewa ba ta san me ya ingiza ta har ta ƙona ‘yar tata ba.
Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole ya ba da umurnin a mayar da matar zuwa sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.
Sai dai, ‘ya sandan ba su sanar da ranar da za su gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu ba.
Cin zarafi ko musguna wa ƙananan yara, babbar matsala ce a Najeriya, inda har yanzu wasu jihohin ƙasar ba su sa hannu kan dokar kare haƙƙin ƙananan yara ba, kuma jihohin da suke da dokar ma, ba kasafai ake jin labarin hukunta masu cin zarafi ko tozarta ƙananan yara ba.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
