Connect with us

News

An daure attajiri kan badakkalar dalar Amurka miliyan 900 a Angola

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Wata kotu a Angola ta yanke hukuncin daurin shekara tara a kurkuku kan Carlos de São Vicente, wani dan kasuwa mai alaka da tsofaffin shugabannin kasar biyu.

Kotun ta daure shi ne kan satar dala miliyan 900, kamar yadda mujallar Novo mai zaman kanta ta ruwaito.

Sai dai lauyoyinsa sun ce za su daukaka kara kan wannan hukuncin.

An tsare Mista De São Vicente na tsawon fiye da shekara guda kafin aka fara shari’arsa watan Fabrairu.

Ya kasaance surukin shugaban Angola na farko Agostinho Neto ne, inda aka mika ma sa ikon gudanar da bangaren man fetur na kasar a karkasshin mulkin shugaba José Eduardo dos Santos.

Advertisement

Amma gwamnati mai ci karkashin shugaba João Lourenço ta maka mutanen da ke da alaka da tsohon shugaban kasar Dos Santos.

Sai dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa na shan suka saboda yadda ake amfani da ita a matsayin makamin siyasa a cikin kasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending