News
APC ta haramtawa masu rike da mukamai kada kuri’a a
Daga maryam Bashir musa
Jam’iyyar APC mai mulki ba za ta bar wadanda suke rike da kujerun siyasa wajen kada kuri’a a zaben shugabanni na kasa da za a gudanar ba.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na Twitter a yammacin jiya Alhamis, 24 ga watan Maris 2022.
A jawabin da jam’iyyar ta fitar, tace masu rike da mukaman gwamnati da aka zaba a matsayin masu kada kuri’a wato delegates, ba za su yi zabe ba.
Kwamitin riko na CECPC ya bada dalilin daukar wannan mataki da cewa akwai ta-cewa game da dokar zabe na kasa, don haka aka hana masu mulki kada kuri’a.
“Kwamitin rikon kwarya da tsara zaben APC ya tsaida cewa duk wadanda ke kan mukaman siyasa da aka zaba a matsayin masu kada a kuri’a a zaben shugabanni da za ayi a 26/3/2022 ba za su yi zabe ba.
“A dalilin sabanin da ake samu a game da sashe na 84 (12) na dokar zabe na shekarar 2022.’
Rahotonni sun ce sashe na 84(10) na wannan doka da majalisar tarayya ta kawo ta hana duk wanda aka ba mukamin siyasa shiga zaben jam’iyya.
Kafin mutum ya iya kada kuri’a a zaben tsaida ‘dan takara, dole sai ya ajiye mukaminsa tukun.
Hakan na zuwa ne duk da wani jigo a jam’iyyar Action Alliance party na kasa, Nduka Edede ya shigar da kara a kotu a Umuahia a kan wannan dokar.
Edede yana ganin sashen wannan doka ya ci karo da wasu bangarorin tsarin mulki na kasa, daga ciki akwai 66(1)(f) 107(1)(f)(137(1)(f) da kuma 182(1)(f).
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da alamu ke nuni da cewa jam’iyyar ta APC na ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shuwagabannin jam’iyyar da ake shirin yi a ranar Asabar mai zuwa.
Tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai daban-daban – inda misali aka kebe wa yankin arewa ta tsakiya kujerar shugaban jam’iyya na kasa.
Haka nan, shugaba Muhammadu Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a wajen zaben shuwagabannin, a maimakon haka a sasanta tsakanin ‘yan takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.
To sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su yarda da wannan tsari ba, misali tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganinsa bai wa wani yanki ko wani mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.
To dazu bayan da gwamnonin jihohi na jam’iyyar ta APC suka gana da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja, shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana cewa, har in ba a samu haɗin kai akan maslaha ba game da yan takara, toh lallai jam’iyyar bata da wani zaɓi illa ta shiga zabe.
