Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta doɗe layukan waɗanda ba su yi rajistarsu ba

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

Gwamnatin Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da ke cikin kasar su hana masu amfanin da layukan tarho yin waya daga layukansu idan har ba su yi rajistarsu ba kuma ba su hada su da lambar zama dan kasa ba (NIN) daga yau Litinin 4 ga watan Afrilun 2022.

Hukumar da ke kula da batutuwan sadarwa a Najeriya NCC tare da hukumar da ke kula da kuma yin rajistar ‘yan Najeriya (NIMC) ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa ta hadin gwuiwa da suka fitar.

Advertisement

Wannan matakin na nufin wadanda aka rufe layukansu saboda rashin hada su da lambar dan kasa ba za su iya kiran kowa ba, sai dai za a iya kiransu.

Ministan sadarwa na kasar Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin.

Advertisement

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kawo yanzu, ta mika lambobin waya miliyan 125 domin a hada su lambar dan kasa, kuma hukumar NIMC ta yi rajistar lambobin dan kasa miliyan 78 kawo yanzu.

Sanarwar ta ce “Muna ba dukkan wadanda aka dode layukansu daga yin waya, da su tafi cibiyoyin da ake yin rajista domin hada lambobin nasu da lambar dan kasa domin kamfanonin sadarwa su iya bude musu layukan nasu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending