News
Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya gargadi al’umman jihar kan amfani da lambar wayarsa ba bisa ka’ida ba.
Daga khadija Abdullahi Mahmud.
Matawalle dai ya ce bayan sakin lambarsa da manufar magance matsalar rashin tsaro a jihar, sai wasu suka fara saka shi a shafukan soshiyal midiya marasa amfani.
Gwamnatin jihar ta ce duk wanda ke da burin amfani da lambar gwamnan a shafi na soshiyal midiya toh ya nemi izini daga ofishin hadiminsa.
Gwamnatin ta gargadi mazauna jihar kan amfani da lambar wayar Gwamna Bello Matawalle ba tare da izini ba.
Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai ba gwamnan shawara ta musamman kan wayar da kan jama’a, Mista Zailani Bappa, a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu.
“Manufar mai girma gwamna na barin lambobin wayarsa su fita cikin al’umma shine domin saka idanu sosai kan lamuran tsaro da kuma lamuran ci gaba daga tushe.
“Ya kuma mayar da shi dabi’a don saka idanu a shafukan soshiyal midiya don jin doriyar mutane da kansa.
“Ya yi hakan ne don ci gaba da bayar da fifiko ga muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba kamar yadda mutane ke muradi.
“Sai dai kuma, wasu mutane masu sakaci suna wofantar da wannan damar ta hanyar saka lambar mai girma gwamna a shafukan soshiyal midiya marasa amfani ba tare da izini ba.”
Ya kuma shawarci jama’a da ke burin saka lambar gwamnan a kowani dandamali na soshiyal midiya da su nemi izini daga ofishin mai bashi shawara na musamman kan wayar da kan jama’a, labarai da sadarwa, rahoton Daily Nigerian.
