Connect with us

News

Rasha ta fara luguden-wuta a Donbas, in ji Zelensky

Published

on

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce Rasha ta kaddamar da wani gagarumin farmaki da aka jima ana sa ran za ta fara kai wa a gabashin kasar.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, ya ce an fara yakin yankin Donbas.

Mista Zelensky ya ce a yanzu da yawa daga cikin sojojin Rasha sun mayar da hankali kan aikin da suka dade suna shiryawa.

Ya ce a zahiri, Rasha na son gamawa da yankin Donbass, su lalata shi, su ruguza duk tarihin da ke wannan yanki na kasuwanci.

Ya kara da cewa dakarun Rasha ke wargaza Moriupol, don haka sun kuduri aniyar takaita rayuwar mutanen Donetsk, da Luhansk da Kharkiv.

A bangare guda, kwamitin tsaron kasar Ukraine ya ce sojojin Rashar na dannawa ta ko ina.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending