Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100 a babban zaɓe na 2023 mai zuwa.
Wani jadawalin gudanar da zaɓukan fid da gwani da jam’iyyar ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwarta a yau Laraba ya nuna cewa masu son yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutar APC za su biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, sai kuma kuɗin fom naira miliyan 70.
Kazalika, masu son yin takarar gwamna za su lale naira miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya miliyan 20.
Masu fatan zama ‘yan majalisar wakilai za su biya naira miliyan 10. Su kuma ‘yan majalisar jiha miliyan biyu.
