Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na halartar taron Majalisar Zartarwa na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar da ke gudana yanzu haka.
Ana gudanar da taron ne a otel ɗin Transcop Hilton da ke Abuja karon farko tun bayan da APC ta zaɓi sabbin shugabanninta a watan Maris.
Ana sa ran ‘yan majalisar wanda Buhari na ɗaya daga cikinsu, za su daddale jadawalin zaɓukan fid da gwani na jam’iyyar a matakin shugaban ƙasa da kuma na jihohi.
Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu…
