Connect with us

News

Yan bindiga sun sace mutum hudu ‘yan gida daya a Abuja

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

Wasu mahara da ake kyautata zaton masu satar mutane domin kudin fansa ne sun afkawa al’ummar Shadadi skuma sun sace mutum hudu da sanyin safiyar Laraba a karamar hukumar Kuje ta Abuja babban birnin Najeriya.

Wasu mazauna yank sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 1 na dare bayan da suka rika harbin mai uwa da wabi domin tsorata mazauna yankin.

Jaridar vanguard ta ruwaito cewa wani dan uwan wandanda aka sace na cewa maharan su goma sun kutsa cikin gidan bayan balla babbar kofar shiga ciki.

Advertisement

Ya nemi jami’an tsaro da su taimaka wajen kwato ‘yan uwan nasa, inda ya ce dukkansu ‘yan uwan juna ne.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending