News
An yanke wutar lantarki a gidan gwamnati saboda bashi
Daga maryam bashir musa
Kamfanin dake raba hasken wutar lantarki (Abuja Electricity Distribution Company) ya katse wutar lantarkin fadar gwamnatin jihar Niger da majalissar dokokin da hukumar ruwan sha da kuma babbar sakatariyar jihar.
Kamfanin ya yanke wutar lantarkin ne biyo bayan bashin naira biliyan daya da miliyan dari bakwai da yake bin gwamnatin jihar ta Niger.
Wannan na zuwa ne watannni kadan bayan da kamfanin samar da wutar lantarki dake Ibadan ya katse wutar lantarkin sakatariyar jihar Oyo.
Sai dai gwamnatin jihar Niger ta musanta batun inda tace ana binta bashin naira biliyan daya da miliyan dari daya ne ba kamar yadda kamfanin ya ambata ba.
Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ibrahim Ahmed Matane, ya musanta batun yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishin sa dake Minna.
Ya ce gwamnatin jihar ta gaji naira miliyan dari uku daga cikin biliyan guda a gwamnatin tsohon gwamnan jihar Mu’azu Babangida Aliyu.
Alhaji Ibrahim Ahmed Matane, ya kuma ce tuni tattaunawa tayi nisa da kamfanin raba wutar lantarkin don dawo da wutar lanatarki a ranar Juma’a mai zuwa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
